IQNA

19:30 - August 28, 2010
Lambar Labari: 1983006

An Buga Littafin Ikmaluddin Ihsan Auglo A Kasar Rasha

Bangaren kasa da kasa; An buga littafin nan mai suna Madina na babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a kasar Rasha, wanda aka buga a cikin harshen rashanci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na idmedia an habarta cewa, an buga littafin nan mai suna Madina na babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a kasar Rasha, wanda aka buga a cikin harshen rashanci domin amfanin musulmin kasar.

Littafin dai ya kunshi bayanan da Auglo yake gabatarwa ne a dukkanin tarukan kungiyar OIC, da kuma jawabansa kan addinin muslunci a taruka daban-daban da aka gudanar a kasashen musulmi kimanin hamsin da bakwai.

642496



captcha