IQNA

An Bude Cibiyar Yada Ayyukan Kur'ani A Morocco

19:30 - August 28, 2010
Lambar Labari: 1983007
Bangaren kasa da kasa; A jiya ne aka bude wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani a birnin Muhammadiyya na kasar Morocco tare da halartar sarkin kasar Muhammad na shida.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Morocco cewa, a jiya ne aka bude wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani a birnin Muhammadiyya na kasar Morocco tare da halartar sarkin kasar Muhammad na shida, da nufin fadda harkokin kur'ani a kasar.

Bayanin ya ci gab ada cewa wannan cibiya za ta mayar da hankali ne wajen kara samar da hanyoyi na bunkasa ayyukan kur'ani a kasar, tare da shirya taruka na gasar harda da karatun kur'ani mai tsarki a sassa daban-daban na kasar.

Wasu daga cikin 'yan asalin kasar da suke zaune a kasashen ketare sun taka gagarumar rawa wajen kafa wannan babbar cibiya.

642448


captcha