Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wata gasar kur'ani ta yanki-yanki da aka saba gudanarwa akasar Faransa, amma a wannan karon a yankin Lyon, wadda za a fara gudanarwa daga ranar Litinin mai zuwa a babban masallacin birnin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Novopress an bayyana cewa, za a gudanar da wata gasar kur'ani ta yanki-yanki da aka saba gudanarwa akasar Faransa, amma a wannan karon a yankin Lyon, wadda za a fara gudanarwa daga ranar Litinin mai zuwa a babban masallacin birnin na Lyon.
Musulmin kasar Faransa dake gudanar da ayyukansu karakshin babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar Faransa, sun saba gudanar da irin wannan gasa a irin wadannan lokuta.
642960