IQNA

Ana Gudanar Da Taruka Kan Kur'ani A Yankin Kutaif

12:37 - August 29, 2010
Lambar Labari: 1983069
Bangaren kasa da kasa; Ana gudanar da taruka kan kur'ani a yankin Kutaif da ke gabacin kasar Saudiyya, wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na yankin suke gudanarwa a kowace shekara da ake baiwa take Imam Ali (AS) kur'ani mai magana.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki a yankin Kutaif cewa, Ana gudanar da taruka kan kur'ani a yankin Kutaif da ke gabacin kasar Saudiyya, wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na yankin suke gudanarwa a kowace shekara da ake baiwa take Imam Ali (AS) kur'ani mai magana ko natik.


Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron yana samun halartar makaranta kur'ani mai tsarki da ma mahardata da suke da sha'awa, inda akan yi karatuka daga bisani kuma a gabatar da jawabai ga mahalarta.

A wannan shekarar tarukan na samun halart daruruwan mutane musamman ma matasa da suke da sha'awar karatun kur'ani, da neman sanin ilmomin da suke kunshe a cikinsa.

642881

captcha