IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Karo Na Tara A Tunisia

11:40 - August 30, 2010
Lambar Labari: 1984110
Bangaren kasa da kasa; A jiya ne aka fara gudanar da gasar hardar kur'ani ta kasa baki daya a kasar Tunisia tare da halartar mahardata kur'ani mai tsarki daga sassa davab-daban na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar shiryawa da gudanar da ayyukan kur'ani ta kasa a Tunisia an habarta cewa, ajiya ne aka fara gudanar da gasar hardar kur'ani ta kasa baki daya a kasar Tunisia tare da halartar mahardata kur'ani mai tsarki daga sassa davab-daban na kasar ta Tunisia.

Rahoton wanda kamfanin dillancin labaran kasar ta Tunisia SPA ya habarta ya yi nuni da cewa shugaban kasar ta Tunusia Zainul abiding bin Ali shi n eke mara wa shirin baya kai tsaye, imda ya ke fatan ganin shirin ya dore kamar aka fara shi.

Taron gasar hardar kur'ani zai samu halartar jami'an gwamnati daga sassa daban-daban na ma'aikatun kasar, kamar yadda wasu daga cikin mambonin majalisar kasar za su halarci zaman taron.

643700



captcha