Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga cibiyar malaman addinin muslunci ta kasar Turkiya mai kula da harkokin fatawa an bayyana cewa, za a gudanar da wani babban taro na kasa da kasa da kasa da aka yi wa take da liyafar kur'ani mai tsarki a kasar Turkiya, wanda za a gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar ta Turkiya.
Taron wanda wanda za a gudanar a cikin watan Ramadan mai alfarma, wanda kuma shi neirinsa na farko, zai samu halartar makaranta daga sassa daban-daban na duniya musamman ma kasashen musulmi.
Taron yana da nasaba da cika shekaru 1400 da safkar wahayin kur'ani mai tsarki, daga cikin wadanda za su halarci taron akwai mahardata daga kasashen Sudn, Iran, Masar da kumaSyria.
643736