Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Amurka mai taken msulunci da musulmi, da za a gudanar a birnin Chicago tare da halartar masana da malaman addini daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oicun an habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Amurka mai taken msulunci da musulmi, da za a gudanar a birnin Chicago tare da halartar masana da malaman addini daga sassa daban-daban na kasar ta Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin wadanda za su halarci akwai wasu manyan baki da aka gayyata daga kasashen musulmi, inda za a gabatar da jawabai.
Jawaban da za a gudanar za su mayar da hanakali kan matsayin siyasar Amurka da kuma duniyar musumi, da hanyoyin day a kamata a bi wajen karfafa ta.
643459