IQNA

Talabijin Din Sweeden Ba Ta Amince Da Yada Kiyayya Ga Musulmi Ba

11:41 - August 30, 2010
Lambar Labari: 1984115
Bangaren kasa da kasa; Wata talabijin din kasar Sweeden ta nuna rashin amincewarta da yada wasu shirye-shirye na kiyayya da addinin musulunci, wadanda jam'iyar masu tsananin gaba da musulunci ta kasar ke shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na risalehaber an bayyana cewa, wata talabijin din kasar Sweeden ta nuna rashin amincewarta da yada wasu shirye-shirye na kiyayya da addinin musulunci, wadanda jam'iyar masu tsananin gaba da musulunci ta kasar ke shiryawa da nufin cin zarafin musulmi.

Jam'iyar mai gaba da addinin musulunci tana yin kamfe da kiyayya ga musulmin kasar ne da nufin samun goyon bayan kungiyyin da suke tsananin gaba da musulunci na kasar ta Sweeden.

Wannan jam'iya ta shirya wasu sanarwoyi da nufin a yada su a wani gidan talabijin din na kasar, amma talabijin din ya ce ba zai taba watsa abin da zai kawo kiyayya ga wani bangaren addini ba.

643694




captcha