Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na press release point an habarta cewa, Za a gudanar da wani taro na nuna kyakkyawan rubutun kur'ani mai tsarki a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa a ci gaba da gudanar da tarukan watan Ramadan mai alfarma kamar yadda yadda aka saba gudanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar masu gudanar da ayyukan fasaha daga kasashen larabawa da na musulmi daban-daban, inda za su nuna irin kayyakin fasarharsu na rubutun kur'ani.
Taron ana gudanar da shi ne bisa hadin gwiwa tasakanin ma'aikatun kula da harkokin addini na kasar da kuma ma'aikatar raya al'adu da ilimi.
645049