IQNA

An Bude Gasar Kur'ani ta Kasa Da Kasa A Masar

9:44 - August 31, 2010
Lambar Labari: 1984721
Bangaren kasa da kasa; An bude gasar kur'ani ta duniya da aka saba gudanarwa a kasar masar tare da halar makaranta kur'ani daga kasashen duniya 68, wadda aka fara gudanarwa abirnin Alkahira fadar mulkin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar kasar Masar ta al-akhbar an bayyana cewa, an bude gasar kur'ani ta duniya da aka saba gudanarwa a kasar masar tare da halar makaranta kur'ani daga kasashen duniya 68, wadda aka fara gudanarwa abirnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar.

A yayin bude taron gasar, wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar sun samu halarta da suka hada fira ministan kasar Ahmad Nazif, sai kuma babban malami mai bayar da fatawa na jami'ar Azhar sheikh Ahmad tayyib.

Haka nan kuma daga cikin wadanda suka halarci taron bude gasar akwai ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Mahmud Hamdi Zaqruq, gami da wasu daga cikin jakadun kasashen duniya.

645039


captcha