Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ummid na yanar gizo cewa, an kammala gasar harda da karatun kur'ani mai tsarki a birnin Mambai na kasar India, tare da halartar mahardata da makaranta kur'ani daga sassa daban-daban na kasar ta India.
Wasu daga cikin cibiyoyi da suke da wasu harkokin addinin Musulunci na kasar ne suka dauki nauyin shirya gudanar da wannan gasa, wadda ta samu halartar mahardata da makaranta kimanin 236 daga garuruwan kasar.
Daga cikin cibiyoyin hard a cibiyar ayyukan alhairi ta birnin Mambai, da kuam cibiyar kula da ayyukan haji, da sauran kungiyoyin musulmi.
644905