Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne daga reshensa da ke hukumar da ke kula da harkokin kur'ani da kusanci a tsakanin kasashen musulmi ya watsa rahoton cewa; A tanzaniya ma kamar yawancin kasashen duniya musamman musulmi za a gudanar da bukin tunanawa da zagayowar ranar Qudus ta duniya ta kowace ranar juma'ar karshe ta watan azumin ramadana mai albarka a masallacin Kicangali na birnin Darul Salam fadar mulkin wannan kasa.A wajen wanna taro za a samu halartar limaman juma'a nay an shi'a da sunnaa Tanzaniya da wakilan kungiyar al'ummar yan shi'a mabiya limamai sha biyu na Tanzaniya TIC da kungiyar al'umma musulmin Tanzaniya TIC da a yan kwanakin nan suka gudanar da tarurruka na bai daya domin shiraya tunkarar wannan babban taro.
645101