IQNA

Kira'ar Sheikh Farjallah Shazili A Hubbaren Abbas (AS)

22:53 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985860
Bangaren kasa da kasa; Fitaccen malamain nan makarancin kur'anin na jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya gudanar da kira'a a hubbaren Abbas (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na Nun na yanar gizo ya habarta cewa, Fitaccen malamain nan makarancin kur'anin na jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya gudanar da kira'a a hubbaren Abbas (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma da ke kasar kasar Iraki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, shehin malamin ya kai ziyara a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin mai alfarma, daga nan kuma sai ya wuce zuwa hubbaren Abul fadhl Abbas (AS) inda ya gudanar da karatun kur'ani da aka watsa kai tsaye.

Malamin ya nuna matukar tasirantuwarsa da ziyarar wadannan wurare masu tsarki da suke birnin Karbala, inda ya yi addu'a na neman tabarruki.

645776







captcha