IQNA

22:55 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985863
Bangaren kasa da kasa; Wasu kasashen musulmi za su bayar da taimakon kudi har dalar Amurka biliyan daya ga gwamnatin kasar Pakistan domin talafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta yi yankan kauna a fadin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran medya73 cewa, wasu kasashen musulmi za su bayar da taimakon kudi har dalar Amurka biliyan daya ga gwamnatin kasar Pakistan domin talafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta yi yankan kauna a fadin kasar ta Pakistan.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin kasashen da suka dauki alkawalin bayar da wannan taimako hard a kasashen saudiyya, Turkiya, Kuwait,Qatar, hadaddiyar daular da kuma wasu daga cikin fitattun 'yan kasuwa na kasashen larabawa.

645677Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: