Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, An gudanar da wani taro kan ayyukan kur'ani a nahiyar Afirka a wurin baje kolin kayyakin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran a kari na goma sha takwas jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya hada wasu daga cikin wakilan cibiyoyin Musulunci na wasu kasashen nahiyar Sfirka ne da suka halarci baje kolin kur'anin, inda wasu daga cikinsu suka kawo nasu samfurin ayyukan.
A zaman taron an tattauna muhimman hanyoyin da za a bi wajen kara bunkasa harkokin kur'ani a kasashen nahiyar Afirka tare da hadin gwiwa da sauran kasashen musulmi.
646459