Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, an sanar da zama na ashirin da daya a baje kolin kur'ani na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, tare da halartar wakilai daga cibiyoyin kur'ani da suke halartar baje kolin na duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a yayain gudanar da zaman wasu daga malamai sun gabatar da jawabai kan mahangar kur'ani mai tsarki dangane da wasu batutuwa da dama da suke da dangantaka da matsayin kur'ani a rayuwar jama'a ta zamantakewa.
Jami'ar Al-Mostafa (SAW) ta duniya ita ce ta jagoranci shirya wannan zama tare da wakilanta da kuma sauran wakilan cibiyoyin addini.
646460