IQNA

An Fara Gudanar Da Tarukan Dararen Ramadan A Spain

13:32 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1986973
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da tarukan dararen watan Ramadan a kasar Spain wanda cibiyar nan ta kabilun larabawa mazauna kasar da ke birnin Madrid ta shirya gudanarwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na map an bayyana cewa, an fara gudanar da tarukan dararen watan Ramadan a kasar Spain wanda cibiyar nan ta kabilun larabawa mazauna kasar da ke birnin Madrid ta shirya gudanarwa daga ranar Alhamis da ta gabata.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan cibiya tana daukar nauyin gudanar da tarukan ne da nufin karfafa musulmi mazauna kasar, musamman ma wadanda suka yi hijira daga wasu kasashe zuwa kasar ta Spain a matsayin masu gudun hijira.

A lokacin gudanar da tarukan a kan gabatar da jawabai da kuma kara karfafa musulmi kan yin riko da koyarwar addinin Musulunci a cikin dukkanin harkokin rayuwa.

647092



captcha