IQNA

Taron Kur'ani Na Alkauthar A Yankin Kutaif Na Saudiyya

13:33 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1986978
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron kur'ani na alkauthar a yankin Kutaif na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar saudiyya a masallacin Zahra (AS) da ke garin Ummul hamam.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na tashar rasid cewa, za a gudanar da taron kur'ani na alkauthar a yankin Kutaif na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar saudiyya a masallacin Zahra (AS) da ke garin Ummul hamam da ke yankin.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanan taron an saba gudanar da shi a kowace shekara da nufin kara karfafa mazuna yankin kan yin aiki da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokinsu na zamantakewar rayuwa.

An gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da ake cikin taruka na makokin shahadar Imam Ali (AS) wanda mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suka saba gudanarwa a yankin.

647006


captcha