IQNA

An Nuna Shafukan Yanar Gizo 400 Na Addini A Baje Kolin Kur'ani

16:25 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1987173
Bangaren kasa da kasa; A wasu bangarori na taron baje kolin kur'ani mai tsarki da aka gudanar a karo na goma sha takwas a birnin Tehran an nuna wasu shafukan yanar gizo 400 dukkaninsu na addini da kuma ayyukan kur'ani.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban bangaren kayyakin addini na hauza da aka nuna a baje kolin kur'ani a wasu bangarori na taron baje kolin kur'ani mai tsarki da aka gudanar a karo na goma sha takwas a birnin Tehran an nuna wasu shafukan yanar gizo 400 dukkaninsu na addini da kuma ayyukan kur'ani mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan shafuka na yanar gizo za su taka gagarumar rawa ne a bangarori daban-daban na addini da nufin kara ilmantar da musulmi kan lamurra da dama da suka danganci addinin Musulunci.

Cibiyar yada ilmomin addinin Musulunci ta hauza ta taka gagarumar rawa wajen samar da shafukan yanar gizo na addini da nufin ilmantar da musulmi ko'in cikin fadin duniya da suka yin amfani da wannan hanya.

646997



captcha