IQNA

ISESCO Za Ta Halarci Taron Cika Shekaru 1400 Da Safkar Wahayi

16:26 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1987175
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adun kasashen musulmi ta ISESCO za ta halarci taron cika shekaru 1400 da safkar wahayi da yanzu haka shirin gudanarwa a kasar Turkiya.


Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar hadin kan kasashen musulmi an bayyana cewa kungiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adun kasashen musulmi ta ISESCO za ta halarci taron cika shekaru 1400 da safkar wahayi da yanzu haka shirin gudanarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro wanda daya ne daga cikin tarukan addinin Musulunci masu matukar muhimmanci da za a gudanar a kasar Turkiya, ya ja hankulan da dama daga cikin kungiyoyi da cibiyoyin addini a kasashe daban-daban, da suka sanar cewa za su halarci zaman taron.

646976



captcha