Bangaren kasa da kasa; An shiga bangare na karshe a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Algeria wadda ake gudanarwa a karo na uku, kuma gidajen talabiji ke watsa ta kai tsaye a lokacin da ake gudanar da ita.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ennaharonline.com an bayyana cewa, an shiga bangare na karshe a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Algeria wadda ake gudanarwa a karo na uku, kuma gidajen talabiji ke watsa ta kai tsaye a lokacin da ake gudanar da ita a dakin taro.
Gasar wadda ta kebanci makarantan kur'ani na cikin kasar ne kawai, tana samun halarta daga sassa daban-daban na kasar, inda makaranta suke karawa da juna a bangarorin karatu da kuma ilmimi sanin kaidar karatun kur'anu mai tsarki wato tajwid.
Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a kowace shekara, kuma ana zabar mutumin da ya fi dukkanin makaranta taka gagarumar a matsayin zakaran gasar.
646977