Bangaren kasa da kasa; An bude wani shafin yanar gizo mai suna Nur hayati domin gudanar da ayyukan kur'ani mai tsarki ta hanayar sadarwa ta internet a kasar Kuwait, da nufin karaffa matasa wajen lamurran kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Ukaz da ake bugawa a kasar Saudiyya ta habarta cewa, an bude wani shafin yanar gizo mai suna Nur hayati domin gudanar da ayyukan kur'ani mai tsarki ta hanayar sadarwa ta internet a kasar Kuwait, da nufin karaffa matasa wajen lamurran kur'ani mai tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa ta wannan hanaya matasa musulmi za su iya yin karatu da harda da kuma sanin ka'idoji na karatun kur'ani mai tsarki, kamar yadda shafin zai rika bayar da bayanai kan wasu ilmomi na addini da suke da dangantaka da tarbiyar matasa musulmi.
Yanzu haka shafin ya fara gudanar da ayyukansa acikin wannan wata na ramadana mai alfarm, kuma ana sa ran zai ci gaba da kara fadada ayyukansa daga lokaci zuwa lokaci.
646953