IQNA

An Shiga Mataki Na Karshe Na Gasar Kur'ani A Turkiya

16:23 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1987181
Bangaren kasa da kasa; An shiga bangaren karshe na gasar karatun kur'ani mai tsarki ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ake gudanarwa a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar zainabiyya cewa, An shiga bangaren karshe na gasar karatun kur'ani mai tsarki ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ake gudanarwa a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya da ke samun halartar makaranta.

Shugaban cibiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah ya bayyana cewa wannan gasa tana daya daga cikin irinta wadanda aka gudanar a kasar Turkiya da suka samu karbuwa daga makaranta daban-daban da suke zuwa daga garuruwan kasar.

Ya ci gaba da cewa yanzu an kammala dukaknin shirye-shiryen kammala gasar bayan shiga bangaren karshe, wanda daga nan ne za a sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar.

646943




captcha