Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wata zanatawa da ta hada wakilinsa da daraktan cibiyar kur'ani ta Nasiriyya Adnan Raad ya bayyana cewa, za a girmama dukkanin wadanda suka gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta Nasiiyya a kasar Iraki a wani zama da za a gudanar da aka yi lakabi da daren kur'ani mai tsarki.
Ya ci gaba da cewa wannan gasa ta hada akasarin makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na lardin Nasiriyya na kasar Iraki, ida suka gudanar da karatu da kuma harda a bangarori da daban-daban na gasar.
Daga karshe an fitar da sunayen wadanda suka lashe gasar a dukkanin bangarorin da aka gudanar da ita, wadanda adadinsu ya kai mutane 25, kuma za a taron girmama su.
647348