Bangaren siyasa da zamantakewa, A daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar ranar Qods a kasar Afghanistan wasu dubban mutanen sun sanya hannu a kan wata takardar yin Allawadai da ayyukan ta'addancin yahudawan sahyuniya kan al'ummar Gaza.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar ranar Qods a kasar Afghanistan, wasu dubban mutanen sun sanya hannu a kan wata takardar yin Allawadai da ayyukan ta'addancin yahudawan sahyuniya kan al'ummar palastinu.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da ayyukan ta'addancin yahudawan sahyuniya a cikin yankunan palastinawa da ke cikin dukkanin yankunan da yahudawan suke mamaye da su.
Haka nan kuma masu jerin gwanon sun yi kira ga dukkanin musulmi da su safke nauyin da rataya kansu na kare masallacin Qods mai alfarma dake karkashin mamamyar yahuwan sahyuniya.
647568