IQNA

Za A Gudanar Da Wani zaman Taron Addini A Birnin Brussel

13:54 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988700
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro na addini da zai yi dubi kan matsayin tuba a addinin Musulunci da kuma matakan da amfaninta ga musulmi a birnin Brussel na kasar Belgium.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic-events cewa, za a gudanar da wani zaman taro na addini da zai yi dubi kan matsayin tuba a addinin Musulunci da kuma matakan da amfaninta ga musulmi a birnin Brussel na kasar Belgium wanda shi ne irinsa na farko.

Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin musulmi ta birnin Brussel din ce ta shirya gudanar da wannan zaman taro, inda malamai za su gabatar da laccoci kan matsayin tuba a mahangar kur'ani da kuma muhimmancinta ga musulmi.

Taron wanda za a gudanar tare da halar wasu daga cikin wakilan kungiyoyin musulmin kasar ya samu karbuwa daga musulmin kasar ta Belgium.

648235


captcha