Bangaren kasa da kasa; An bude bangaren nazarin kur'ani mai tsarki a jami'ar birnin Karbala mai alfarma, da kuma nazarin wasu ilmomin addinin muslunci da suka hada da ilmin sanin shari'a da kuma usul.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun cewa, an bude bangaren nazarin kur'ani mai tsarki a jami'ar birnin Karbala mai alfarma, da kuma nazarin wasu ilmomin addinin muslunci da suka hada da ilmin sanin shari'a da kuma usul da wasu ilmomin na daban.
Rahoton ya ce yanzu haka kimanin dalibai 200 suka yi rijista a bangaren gudanar da wannan nazari a cikin jami'ar birnin Karbala, inda, za a wadata bangaren da dukkanin littafan da ake bukata domin bayar da dama ga masu gudanar da nazari su samu littafan bincike.
648257