Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da bangaren yada labaransa na kasar Lebanan ya bayar an bayyana cewa, babbar majami'ar kiristocin kasar Syria ta yi Allawadai da kiran da wasu masu tsananin gaba da addinin Musulunci suka yi a kasar Amurka da a mayar da ranar 11 ga watan satumba ta zama ranar kone kur'ani ta duniya a Amurka da sauran kasashen turai.
A cikin wani bayani da babbar majami'ar ta Syria ta fitar ta bayyana kiran da Terry Jones shugaban majami'ar masu tsattsauran ra'ayi kiristanci ta Amurka ya yi, da ke kira a mayar da ranar 11 ga wata satumba ta zama kone kur'ani ta duniya, hakan ya saba wa koyarwa addinin kirista.
Jawabin ya yi Allawadai da matakin na majami'ar Terry Jones, tare da duk wadanda suka goyi bayan hakan a kouna suke cikin fadin duniya, tare da bayana su a matsayinsu masu wakiltar kansu ba addinin kiristanci ba.
648545