IQNA

Zaman Taro Kan Ayyukan Haji A Kasar Faransa

10:39 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989311
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman taro kan ayyukan haji a kasar, wanda cibiyar kula da ayyukan haji ta kasar da ke da babban ofishinta abirnin paris fadar mulkin kasar ta dauki nauyin shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na saphirnews an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro kan ayyukan haji a kasar, wanda cibiyar kula da ayyukan haji ta kasar da ke da babban ofishinta abirnin paris fadar mulkin kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, babbar manufar gudanar da wannan zaman taro dai ita ce bayar da horo ga masu niyar zuwa ayyukan haji, domin sanin yadda ake gudanar da aikin bisa koyarwa ta addini, tare da sanin hukunce-hukunce.

Za a fara gudanar da zaman ne daga makonni biyu masu, tare da halartar wasu daga cikin malamai masu koyar musulmin kasar Faransa ilmomin addinin Musulunci.

649206




captcha