Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Daily Times da ake bugawa a kasar Pakistan an bayyana cewa, an fara gudanar da wani taron baje koli na kayayyakin rubutun Musulunci na shekarar 2010 a kasar Pakistan, wanda yanzu haka yake gudana a birnin Islamabad fadar mulkin kasar ta Pakistan.
Yanzu haka dai ana nuna wasu daga kayayyaki na fasahar Musulunci da suka kai adadi 150, da kuma wasu manyan alluna da suke dauke da rubuce-rubucen Musulunci, wadanda wasu daga cikin fitattun musulmin kasar ta Pakistan suka rubuta a wannan zamani da kuma daddu daga cikinsu.
649523