IQNA

Babban Malamin Kirista A Milan Ya Bukaci A Gina Masallaci

13:47 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989665
Bangaren kasa da kasa; Babban malamin addinin kirista na birnin Milan a kasar Italia ya bukaci da agina masallaci a cikin birnin, inda ya bayyana hakan da cewa hakkin musulmi ne su samu wuraren ibadarsu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga jaridar zaman ta kasar Turkiya an habarta cewa, babban malamin addinin kirista na birnin Milan a kasar Italia ya bukaci da agina masallaci a cikin birnin, inda ya bayyana hakan da cewa hakkin musulmi ne su samu wuraren ibadarsu ba tare da tauye hakkokinsu ba.

Wannan kira ya z one a daidai lokacin da musulmin birnin suke kokawa a musamamn ma a lokutan Ramadan, sakamakon rashin masallatan da za su gudanar da sallar jama'a, wanda hakan ke ci musu tuwo a kwarya.

Musulmin sun kai kuka ga mahukunta inda aka bukaci jin tab akin manayan malaman addinin kirista na birnin, daga bisani kuma suka nuna amincewarsu.

649449



captcha