IQNA

Kasashe 8 Ne Ke Halartar Taron Bude Na Musulunci A Malazia

13:48 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989669
Bangaren kasa da kasa; Kasashe takwas ne daga sassa na duniya suke halartar taron yawon bude na Musulunci a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar malazia, da nufin fadada ayyukan bude a kasashen musulmi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafn sadarwa na All voices cewa, kasashe takwas ne daga sassa na duniya suke halartar taron yawon bude na Musulunci a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar malazia, da nufin fadada ayyukan bude a kasashen musulmi daban-daban.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro cibiyar bunkasa harkokin yawon bude ta kasashen musulmi da ke karkashin kulawar ma'aikatar kula da harkokin yawon bude ido ta Malazia ta dauki nauyin shirya shi.

Manufar taron dai ita ce samar da hanyoyin da za su bayar da dama bunkasa irin wadannan harkoki na bude ido, inda aka sanar da wasu daga cikin irin shirye-shiryen da wannan cibiya take da su.

649316



captcha