IQNA

Za A Kafa Bankin Musulunci Na Farko A Kasar Ethiopia

13:03 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990462
Bangaren kasa da kasa; Za a kafa bankin Musulunci a kasar Ethiopia ta hanyar babban bankin kasar da nufin kara bunkasa harkokin banki da jawo saka hannayen jarukan musulmi.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na casefree an bayyana cewa, za a kafa bankin Musulunci a kasar Ethiopia ta hanyar babban bankin kasar da nufin kara bunkasa harkokin banki da jawo saka hannayen jarukan musulmi a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan banki zai gudanar da ayyukansa ne daidai da koyarwa irin ta shari'ar Musulunci da kuma ka'idoji da dokoki, ta yadda za a iya aiwatar da dukkanin ayyukansa ba tare da saba ka'idojin ba.

Bankunan kasar da dama da suke fuskantar matsaloli sun fara daukar matakan kalubalantar wannan banki a kasar, domin kuwa sun yi amanar cewa zai kwashi jama'a.

650480



captcha