Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Kimanin masallatai 696 za a gudanar da sallolin idi a cikinsu a fadin kasar hadaddiyar daular larabawa da hakan ya hada da manyan biranan da kuma kanan garuruwan kasar.
Rahoton ya kara da cewa yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shirye na na masallatan, inda aka kammala wadanda ake cikin ginawa, da kuma gyaran wadanda ake cikin gyaransu.
Daga cikin masallatan 209 duk suna cikin birnin Abu Dhabi ne, 85 kuma suna cikin birnin Bani yas, 123 kuma a birnin Sharjah, sauran kuma suna cikin Dubai da sauran yankunan kasar.
649593