Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, magajin garin birnin Rom na kasar Italia tare da wasu jami'an gwamnati sun halarci wani buda baki da musulmi suka shirya a birnin na Rom.
Bayanin ya ci gaba da cewa magajin garin na Rom Jani Almano tare da wasu malaman addinin msulunci da wakilan cibiyoin musulmi na kasar Italia sun zauna tare a lokacin gudanar da wannan buda baki.
Babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin Rom ita ce ta dauki nauyin shirya wannan buda baki, tare da gayyatar jama'a.
650278