IQNA

Musulmin Kasar Afghanistan Sun Yi Kira Da A Kare Kur'ani

13:25 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990469
Bangaren kasa da kasa; Daruruwan musulmi ne a kasar Afghanistan suka gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da hankoron kona kur'ani da wasu tsagerun kiristoci ke neman yi a kasar Amurka.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na lefigaro cewa, daruruwan musulmi ne a kasar Afghanistan suka gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da hankoron kona kur'ani da wasu tsagerun kiristoci ke neman yi a kasar Amurka a ranar 11 ga watan satumba.

Daruruwan musulmin sun gudanar da zanga-zanga ne a cikin birnin Kabul, inda suka bukaci da a dauki dukkanin matakan da suka dace domin takawa Amurkawa burki kan hankoron da suke yi na kone kur'ani mai tsarki.

650307




captcha