IQNA

Taron 'Yan Shi'a Na Farko Na Kur'ani A Yankin Kutaif

13:25 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990472
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro wanda shi ne irinsa na farko da mabiya mazhabar shi'a na yankin Kutaif a kasar Saudiyya za su gudanar kan kur'ani, tare da halartar malamai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid cewa, za a gudanar da wani zaman taro wanda shi ne irinsa na farko da mabiya mazhabar shi'a na yankin Kutaif a kasar Saudiyya za su gudanar kan kur'ani, tare da halartar malaman addinin musulunci.

Wannan zaman taro na karatun kur'ani ne tsantsa, inda wasu daga cikin fitattun makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na yankin za su hallara, kuma za su gabatar da karatu.

Daga cikin makarantan hard a wadanda suka shahara a karatukan gasar kur'ani da ake yi a sassa daban-daban na duniya.

650294










captcha