Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Aljazeera net cewa makarancin kur'anin nan dan kasar Morocco mai karancin shekaru ya lashe gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Qatar da ta kebanci kanan yara a matsayi na kasa da kasa.
Shafin ya bayyana cewa wannan matashi ya taka gagarumar rawa wajen gudanar da karatu bisa ka'idoji na tajwidi, wanda hakan ya sanya dukkanin masu gudanar da alkalanci a gasar suka amince da cewa ya lashe gasar a bangaren tajwidi.
Wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa sun halarci wannan gasar kur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Qatar.
650202