IQNA

An Bude Wata Cibiyar Musulunci A Kasar Brundi

13:02 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990474
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiyar addinin Musulunci a birnin Ruyigi na kasar Brundi da nufin kara bunkasa harkokin addini a kasar.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya samu daga shafin sadarwa na AMAI cewa, An bude wata cibiyar addinin Musulunci a birnin Ruyigi na kasar Brundi da nufin kara bunkasa harkokin addini a kasar ta Brundi.

An bude wannan cibiya a kusa da babban masallacin birnin tare da halartar malaman addinin Musulunci na kasar da kuma wakilan kungiyoyi daban-daban, gami da wasu daga cikin mutanen gari.

Wannan cibiya za ta mayar da hankali wajen bunkasa ayyuakn Musulunci da kuma yada ilmi ga musulmin kasar, tare da wayar da kan sauran mutanen kan manufofin addinin Musulunci.

650167

captcha