IQNA

Cibiyar Kusanto Da Mazhabobin Musulunci Ta Bude Tashar Talabijin

11:23 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990984
Bangaren kasa da kasa; Babbar cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci ta duniya ta bude wata tashar talabijin da za ta rika watsa shirye-shirye kan tauraron dan adam a cikin harshen larabci adaga kasar Iraki.



Kamfanin dillancn labaran iqna ya habarta cewa, babbar cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci ta duniya ta bude wata tashar talabijin da za ta rika watsa shirye-shirye kan tauraron dan adam a cikin harshen larabci daga kasar Iraki a matsayin gwaji.

Wannan tasha mai suna wahdah za ta rika gudanar da shirye-shirye na addinin muslunci da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinin Musulunci, da mazhabobinsu daban-daban.

Daga cikin shirye-shiyen kuwa har gayyatar malamai daga banagarori daban-daban domin gabatar da bayanai ga musulmi, da nufin samun hadin kai mai dorewa tsakanin wannan al'umma.

651227

captcha