IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Kur'ani A UAE

11:23 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990985
Bangaren kasa da kasa; An girmama wadanda suka gudanar da gasar kur'ani ta Mu'alla a garin ummul kawin da ke cikin kasar hadaddiyar daular larabawa tare da halartar wasu daga cikin mahukuntan birnin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa WAM an bayyana cewa, an girmama wadanda suka gudanar da gasar kur'ani ta Mu'alla a garin ummul kawin da ke cikin kasar hadaddiyar daular larabawa tare da halartar wasu daga cikin mahukuntan birnin na ummul kaun.

Dukkanin wadanda suka gudanar da gasar adadinsu mutane 90, da suka hada da wasu larabawa da suka fito daga wasu sassa na birnin, inda aka ba su kyautuka na musamamn daga sarkin hadaddiyar daular larabawa.

651132


captcha