IQNA

Vatican Ta Yi Allawadai Da Ayyana Ranar Kone Kur'ani

11:24 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990986
Bangaren kasa da kasa; Fadar Vatican da ke kasar Italia ta yi allawadai da ayyna ranar kone kur'ani mai tsarki da wata majami'ar kiristoci masu tsatsuran ra'ayin addini da kiyayya da Musulunci ta yi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar Faransa na AFP an habarta cewa, fadar Vatican da ke kasar Italia ta yi allawadai da ayyna ranar kone kur'ani mai tsarki da wata majami'ar kiristoci masu tsatsuran ra'ayin addini da kiyayya da Musulunci ta yi da nufin tsokanar musulmi.

Fadar Vatikan ta bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar da ke yin allawadai da kudirin majami'ar Florida na ayyana ranar goma sha daya ga watan satumba, a matsayin ranar kone kur'ani mai tsarki ta duniya.

Vatican ta nuna matakin a matsayin wata makarkashiya ga addinin kirista daga wasu mutane da suke raya su kiristoci ne, domin hakan ya yi hannun riga da koyarwar addinin kiristanci.

651060

captcha