Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na ic-el cewa, babbar cibiyar Musulunci ta kasar Birtaniya ta shirya gudanar da wani zaman taro da nufin kara fayyace wa musulmi hakikanin abin da ake nufi da imani da kuma riko da akidar Musulunci ga musulmin kasar.
Wannan zaman taron zai samu halartar wasu masana da kuma malaman addinin muslunci mazauna birnin London, inda za a gabatar da jawabai ga mahalarta, da suka hada da musulmin birnin da kuma wadanda za su halarta daga wasu biranan kasar Birtaniya.
Bayanin y ace gudanar da irin wannan taro yana da matukar muhimmanci, domin kuwa zai zama tamkar hannuka mai sanda ga musulmi mazauna kasar Birtaniya.
651033