IQNA

An Nuna Kur'ani Mai Tarjama Da Harsunan Turanci Da Faransanci

11:22 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990988
Bangaren kasa da kasa; An nuna wani kur'ani da aka tarjama a cikin harsunan turancin ingishi da kuma faransanci a birnin Ajman na kasar hadaddiyar daular a ranar da ta gabata.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa wam cewa, An nuna wani kur'ani da aka tarjama a cikin harsunan turancin ingishi da kuma faransanci a birnin Ajman na kasar hadaddiyar daular a jiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa taron nuna kur'anin ya samu halartar wasu daga cikin mahukuntan yankin, da suka hada da shugabannin bangarorin kula da harkokin addini karkashin ma'aikatar aukaf ta kasar.

Kur'anin dai an yi amfani da hanyoyi na zamani wajen tarjamarsa, ta yadda mai karatu zai iya sanin ma'anonin wasu kalmomi na larabci a lokacin da yake karanta tarjama.

651596

captcha