IQNA

An Kafa Kwamitin Duba Watan Shawal A Birnin Abu Dhabi

11:21 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990989
Bangaren kasa da kasa; An kafa wani kwamiti a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa da zai duba watan shawal, wanda ministan shari'a na kasar ya dauki nauyin kafawa da kula da ayyukan da zai gudanar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar UAE an habarta cewa, an kafa wani kwamiti a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa da zai duba watan shawal, wanda ministan shari'a na kasar ya dauki nauyin kafawa da kula da ayyukan da zai gudanar a yau.

Bayanin ya kara da cewa wannan kwamiti zai mayar da hanakali ne wajen duba watan shawal domin samun masaniya kan tsayawarsa, kuma aikin kwamitin ne ya sanar da mahukunta bayanin gani ko rashin ganin wata.

Kwamitin zai iya tura mambobinsa su duba, kamar yadda kuma yake da damar ya karbi bayanai daga mutane daidaiku da suke duba wata.

651559





captcha