Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya samu daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar tawafuk watani a Kuwai, an bayyana cewa gwamnatin Kuwait ta taya dukkanin musulmi murnar sallah karama a cikin wani bayani da ofishin kula da harkokin addini na kasar ya fitar.
Bayanin ya kara da cew wannan sako yana tattare da taya musulmi murnar salla ne da kuma kammala azumin watan Ramadan mai alfarma, tare da yin fatan alkhairi ga dukkanin musulmi da kuma rokon Allah ya karba dukkanin ayyukan ibadar da suka yi a cikin wannan wata.
Wannan cibiya dai tana daya daga cikin cibiyoyin Musulunci na kasar Kuwait da suke isar da sakonni na addini daga bangaren gwamnati zuwa ga jama'a.
651610