Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da wasu daga cikin mabiya addininin kirista, akakkin kwamitin kula da ayyukan wata majami'a mabiya addinin kirista a Amurka ya bayyana cewa, wulakanta kur'ani babban cin zarafi ga shi kansa Annabi Isa (AS) ne.
Ya ce hankoron da wani shugaban wata majami'a ke yi a cikin jahar Florida da son kone kur'ani mai tsarki, bay a wakiltar mabia addinin kirista, kuma yin hakan ba wai cin zarafin musulmi ba ne kamar yadda yake zato, a'a cin zarafin shi kansa addinin kiristanci ne.
Tun bayan da mutumin mai tsananin gaba da addinin Musulunci ya yi kira da mayar da ranar 11 ga watan satumba na kowace shekara ranar kone kur'ani yake ta fuskantar la'anta daga musulmi da kiristoci da ma al'ummomin duniya.
651418