A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da shugaban jami'ar Al-mostafa ta duniya Alireza A'arafi ya bayyana cewa kone kur'ani mai tsarki da wasu tsiraru masu tsatsauran ra'ayi suke so su yi a Amurka shelanta yaki ne kan al'ummar musulmi na duniya.
Ya ce mutahnen da suke son su aiwara da wannan mummunan aiki dole su san cewa abin da suke son yi yana tattare da gagarumin hadari ga zaman lafiyar duniya ba wai kawai kasar da suke zaune a cikinta ba.
Domin kuwa a cewarsa a ddinin Musulunci shi ne addini na biyu a duniya, a kan haka ya ce yana ganin masu wanan mafarki ma ba za su taba gigin yin hakan ba.
652072