Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Rasha an habarta cewa, za a nuna wasu daga cikin fina-finan Musulunci a baje kolin fim na kasa da kasa da za a gudanar a kasar Tataria a babban birnin kasar.
Wannan baje koli na fina-finan addinin Musulunci dai za afara gudanar da shi daga cikin mako mai zuwa, wanda za a gudanar a matsayi na kasa da kasa da zai samu halartar cibiyoyin fina-finai da dam adaga kasashen musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa bugu da kari kuma za anuna wasu daga cikin fina-finan da akan yi a kan kasashen musulmi wadanda suke koyar da darussa na rayuwar Musulunci.
651702