Bangaren kasa da kasa; Ana shirin gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan harkokin banki a mahangar addinin muslunci a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, tare da halartar jami'an harkokin kudi na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alwasat ta kasar Bahrain an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan harkokin banki a mahangar addinin muslunci a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, tare da halartar jami'an harkokin kudi na kasashen musulmi da kuma na larabawa.
Bayanin ya ce wannan taro za a fara gudanar da shi makonni biyu masu, tare da halartar jami'an harkokin kudi da bankuna na kasashe 50 da suka hada da na musulmi da ma wasu wadanda ba na musulmi ba.
Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce gudanar da bahasi kan mahangar Musulunci dangane da harkokin banki, da kuma yadda za a yi ammfanin da wannan mahangar a cikin harkokin kudu na duniya.
651676